Talata 22 Satumba 2026 - 17:13
Ayatullah Shubairi Zanjani Babban Malami ne Mai Zurfin Bincike da Hangen Nesa

Hauza/ Jagoran juyin juya halin Musulunci ya mika sakon ta’aziyyarsa bisa rasuwar Ayatullah Sayyid Musa Shubairi Zanjani (Allah Ya jikansa), fitaccen malamin Fikihu kuma daya daga cikin manyan masu bincike a fagen ilimin Shi’a.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene’i ya fitar da sakon ta’aziyya bisa rasuwar Ayatullah Sayyid Musa Shubairi Zanjani (Allah Ya jikansa), inda ya bayyana shi a matsayin babban malami, masani kuma mai zurfin bincike da hangen nesa.

Ga fassarar cikakken sakon:

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai.

Mun samu labarin rasuwar babban malaminmu, fitaccen Faƙihi, Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani (Allah Ya jikansa). Wannan babban malami ya shafe tsawon rayuwarsa, ban da ’yan shekarun farko na yarintarsa, yana kan hanyar neman ilimi, koyarwa da bincike. A tsawon lokaci, malamai masu shekarunsa da wadanda suka yi karatu a zamaninsa, da kuma malamansa, sun kasance suna kallonsa a matsayin masani mai zurfin bincike da hangen nesa.

Kwarewarsa a fannoni daban-daban da suka shafi istinbadi da fitar da hukunce-hukuncen Shari’a ta kasance tare da kula da sirrika da kuma zurfafa nazarin kananan bayanai. Majalisun darasinsa, hatta a lokacin da adadin wadanda suke halarta bai wuce wasu ’yan kalilan ba, sun shahara da kasancewa majalisun bincike da zurfafa nazari, kuma hakika haka lamarin yake.

Alhamdulillah, a cikin sama da shekaru talatin da suka gabata, mutane da dama sun samu wannan dama ta amfana da wannan babbar ni’ima ta kasancewarsa, gwargwadon karfinsu, tare da daukar abin da za su yi amfani da shi a cibiyoyin ilimi da wuraren koyarwarsu.

Zama tare da shi ya kasance zaman koyarwa da koyo, hatta a lokacin da yake tafiya a kafa bayan darasi zuwa gidansa mai albarka. Baya ga matsayin iliminsa da aka tabbatar, halayensa na tawali’u da kuma yadda yake mu’amala da dalibai da malamai cikin yanayi irin na uba, abu ne da kowa yake iya gani kuma abin koyi ne.

Babu shakka, rashin wannan fitaccen mutum ya haifar da gibi a jerin manyan masu bincike na matakin farko a tsakanin malaman Shi’a na wannan zamani, wanda watakila zai dauki lokaci mai tsawo kafin a iya cike gibin.

Ina mika ta’aziyyata bisa wannan babban rashi ga Maulanmu, Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), da dukkan Hauzozin Ilimi, musamman dalibansa da masu kaunarsa, sannan musamman ga iyalansa masu daraja, wadanda suka kasance iyali mai tarbiyyar malamai da masana.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka darajarsa.

Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i

31 ga Shahriwar 1405 (22 ga Satumba, 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha